fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Shin da gaske shugaba Buhari ya baiwa Pasto Tunde Bakare tallafin Naira Miliyan 5 ya gina coci? Ji bayani dalla-dalla

Tsohon abokin takarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  watau Fastor Tinde Bakare na shan caccaka kan karbar bashin banki na Naira Biliyan 9 ya gina coci.

 

Gidajen jaridu da yawa sun ruwaito lamarin wanda yake naman zama abin kunya ga faston.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa, Fasto bakare ya aro bashin ne daga bankin Wema Bank.

Wasu kuma sun ce ya aro kudinne daga bankuna 5.

Saidai wani sabon rahoto dakw fitowa shine me cewa shugaba Buhari ya baiwa Fasto Tunde Bakare tallafin Naira Miliyan 5 a yayin da yake gina cocin tasa dake Legas.

Karanta wannan  Labari me dadi: An kwato buhunan takin zamani da 'yan ta'adda suka siya dan hada bamabamai

 

Majiyoyin da suka ruwaito da labarin tallafin da shugaba Buharin ya baiwa Fasto Bakare basu da karfi.

 

Amma da yake ana tsaka da labarin cin bashin Tunde Bakaren ne, maganar na ta yaduwa.

 

Zuwa yanzu dai shi fasto Tunde Bakare bai ce komai ba game da wannan lamari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.