Saturday, July 20
Shadow

Shin matakan tsuke bakin aljihun CBN na tasiri wajen rage hauhawar farashin kaya a Najeriya?

Bankin duniya ya bayyana damuwa tare da kokwanto game da irin matakan tsuke bakin aljihu da babban bankin Najeriya yake dauka, domin shawo kan matsalar hauhawar tashin farashin kayayyaki da kasar ke fama da shi.

Cikin wani rahoto da bankin ya fitar, ya ce duk da irin matakan da Babban Bankin Najeriya CBN ke dauka kamar kara kudin ruwa a bankuna, har yanzu bata sauya zani ba.

Tuni dai masana tattalin arziki a Najeriya suka fara tsokaci kan rahoton Bankin Duniyar.

Dakta Murtala Abdullahi Kwara, masanin tattalin arziki ne, ya shaida wa BBC cewa, Bankin Duniya ya san da ma duk wasu tsare tsare da matakai da CBN ke dauka ba lallai su yi tasiri wajen magance hauhawar farashin kayayyaki ba.

Karanta Wannan  Sunaye masu dadi na maza da mata

Ya ce,”Dalilin da ya janyo haka kuwa shi ne kusan rabin tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne a kan kasashen waje wato sai an canja dala sannan a siyo kayan masarufi.”

“Idan har ba a toshe hanyoyin da kudaden Najeriya ke salwanta ba, to za a ci gaba da fuskantar matsala sosai kuma babu yadda za a yi a rabu da matsalar hauhawar farashin kayayyaki.”In ji shi.

Dakta Murtala Abdullahi Kwara, ya ce wata matsalar da ta ke kara hauhawar farashin kayayyaki itace, idan har za a rinka samun wadanda duk tsadar kaya zasu iya siya, to ba za a taba samun sauki ba, dole sai an samu daidaito.

Karanta Wannan  Jajirtaccen Dan Sanda DCP Abubakar Guri Ya Rasu

Ya ce, “Akwai hanyar da ya kamata a bi domin shawo matsalar hauhawar farashin kayayyakin, duba hanyar da za a shawo kan matsalar faduwar darajar naira, idan har aka farfado da darajar kudin Najeriyar, to kusan komai zai zo da sauki.”

Masanin tattalin arzikin ya ce, dole sai an cire son rai an kuma cire cin hanci da rashawa, sannan gwamnati ta fiddo da tsare-tsaren da za a taimaki masana’antu, a samar da aikin yi, to a nan ne za a samu saukin wannan matsala ta hauhawar farashin kayayyaki.

Bankin Duniya dai na ganin da wuya a cimma muradun da ake bukata yadda suka kamata.

Karyewar darajar kuɗin Najeriya na daga cikin batutuwan da ake alaƙantawa da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Karanta Wannan  Cikin Lumana Muka Yi Zaɓen 2019 Amma Aka Ƙirƙiro Mana Inkwankulusib, Céwar Ja'afar Ja'afar

Najeriya dai na daga cikin kasashen da suka dogara da shigo da kayyakin amfani irin su motoci da tufafi da sauran kayayyakin laturoni, kuma dole idan za a shiga da irin wadannan kayayyaki ana buƙatar canjin kuɗin ƙasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *