
Abu Dajanah a koda Yaushe ya kasance ya kan yi Sallah a bayan Annabi (SAW), amma da zarar ga idar da Sallah cikin sauri sai ya tashi ya fita daga masallaci (ba tare da ya tsaya ya yi addu’a ba).Ana haka sai Annabi (Saww) Ya lura da wannan abu da yake, wata rana bayan gama Sallah sai ya tashi cikin sauri zai fita amma sai Annabi (Saww) Ya hana shi.
Annabi (Saww) Ya tambaye shi, Abu Dajana, halan baka da bukatar komai a wajen Allah (SWT)? Sai Abu Dajana yace: “Ya ma’aikin Allah, Hakika Ina da bukatoci. Ba zan iya komai ba ba tare da Allah ba, koda kyaftawar ido.
Sai Annabi (Saww) yace, “to me yasa baka tsayawa a tare damu bayan idar da sallah ka roki bukatarka?”
Sai Abu Dajana yace, “Ya Ma’aikin Allah (Saww), Hakika ina da wata makwafciya bayahudiya, Wacce take da iccen dabino a gidanta, to wani sashe daga dabinon ya karkato zuwa gidana.”
Abu Dajana ya ci gaba da cewa, “A duk lokacin da iska ta kad’a da dare ‘ya’yan dabinon sukan zubo a gidana, shi yasa kake ganin na tashi da sauri na fita daga masallachi, domin in samu damar tsince ‘ya’yan dabinon in mayarwa mai shi, kafin ‘ya’yana su tashi daga bacci .”
Abu Dajana ya ci gaba da cewa, “Saboda idan suka tashi suka gan shi za su ci, ina yi ma rantsuwa da Allah, ya Ma’aikin Allah, a kwai lokacin da naga ‘daya daga cikin ‘ya’yana yana cin wannan dabinon, a haka na saka ya tsana a cikin makogwaronsa na saka shi ya amaye shi.”
“Lokacin da d’an nawa yayi kuka Sai nace dashi, “Ashe kai ba zaka ji kunya ba ka tashi a gaban Allah (Swt), kana matsayin barawo?”
Lokacin da Sayyidina Abubakar (rta) ya ji haka, sai ya je wajen matar ya sayawa Abu Dajana da iyalinsa wannan iccen dabinon.
Lokacin da wannan Bayahudiyar ta ji wannan irin taka tsantsan din da wannan bawan Allah Abu Dajana yake, kuma ta ji irin kirkin Sayyidina Abubuakar na saya masa wannan iccen na dabinon saboda zamansu a addini daya domin ya karfafa shi.
Nan take suka je ita da ‘ya’yanta taje wajen Annabi (Saww), suka karbi musulunci ta dalilin amanar Abu Dajana.
Musulunci Addini ne wayayye mai son zaman lafiya tare da baiwa kowa hakkinsa.
rariya