Shine Musulmi Dan Bangan Da Ya Yi Batanci Ga Annabi A Abuja Aka Aika Shi Garin Da Ba A Dawowa (Barzahu).
Lamarin wanda ya auku a Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata a yankin Lugbe dake Abuja, an ce dan bangan ya kama wani mai laifi ne sai ake ba shi hakuri da ya sake shi, sai ya furta cewa ‘ko Annabi SAW ne ya zo ya ba shi hakuri ba zai saki mai kaifin ba. Wanda hakan ya fusata matasa musulmai suka bi shi har ofishinsu na ‘yan banga suka fito da shi suka kona.