Sanata Shehu Sani, Sanata me wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijai ya bayyana cewa shirin fim din turanci da Rahama Sadau tare da Yakubu Muhammad da Maryam Booth suka fito a ciki me suna Son of the Caliphate ya birgeshi.
Sanata Shehu Sani ya bayyana hakane a dandalinshi na shafin Twitter inda yace “wannan shirin fim ne me kyau, karka bari a baka labari”
Bayan da Shehu Sanin ya bayyana ra’ayinshi akan fim din Rahamar ta godemai da wannan abu da yayi.