fbpx
Tuesday, December 1
Shadow

Shugaba Buhari baya tsoma baki a ayyukan NNPC – Mele Kyari

Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Malam Mele Kyari, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai taba tsoma baki a cikin ayyukan Kamfanin ba.

Haka zalika ya bayyana cewa, kamfanin  na da cikakken goyon baya daga shugaban kasa wajan gudanar da ayyukan kamfanin yadda ya kamata.

Kyari ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja.

Kamar yadda ya bayyana da cewa, “Ya shafe tsawan shekaru 26 a ma’aikatar, inda yayi  aiki da manayan shugabanin Ma’aikatar tsawan shekaru 15, amma a cewar sa bai  taba ganin shugaban da baya ka tsalanadan  a al’amuran Ma’aikatar ba kamar shugaba Buhari. Inji shi.

Shugaban ma’aikatar man na kasa yace, kamfanin ya mayar da hankali ne kan bunkasa iskar gas a matsayin wata babbar hanyar samar da makamashi domin taimakwa kasar fita daga matsalar wutar lantarki.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *