Dazune shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da tawagarshi data hada da Gwamnonin Bauchi dana Akwa-Ibom da jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu suka tafi kasar Kwadebuwa, inda shugaban zai halarci taron gamayyar kungiyoyin kasashen Afrika dana turai.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kamar yanda wata sanarwa da me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin watsa labarai Femi Adesina ya fitar jiya, shugaban zaiyi amfani da wannan dama dan tabbatar da kasancewar Najeriya cikin shiri somin kawar da matsalolin tsaro da zaman lafiya da nahiyar ta Afrika ke fama dasu.
Muna fatan Allah ya kaisu ya kuma dawo dasu lafiya.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});