fbpx
Monday, June 27
Shadow

Ta tabbatadai: Shugaba Buhari Lawal yake son ya ga ya zama dan takarar shugaban kasa na APC

Rahotanni sun bayyana a fili cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari Ahmad Lawal yake son yaga ya zama shugaban kasar Najeriya.

 

Wata majiya ce ta gayawa jaridar Daily Post haka kuma hakan na zuwane bayan da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zabi Sanata Ahmad Lawal a matsayin zabinsa.

 

Wasu jiga-jigan APC sun bayyana damuwa da goyon bayan da Sanata Abdullahi Adamu ya nunawa Ahmad Lawalne musamman bayan da gwamnonin Arewa suka yanke shawarar goyawa dan kudu baya ya zama dan takarar shugaban kasa a APC.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Gwamna Matawalle ya bayar da umurni a kulle kasuwanni kuma a daina tuka babura da sayar da man fetur a kananun hukumomi biyu na jihar Zamfara

 

Majiyar ta dailypost tace babu yanda za’ayi shugaban APC, Abdullahi Adamu ya fito ya fadi wannan maganar ba tare da sanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

 

Majiya ta kara da cewa, Abdullahi Adamu shine zabin shugaba Buhari a zaben da aka yi na samar da shugaban jam’iyyar saboda haka duk maganar da zai yi da sa bakin shugaban kasar zai yi ta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.