fbpx
Monday, August 8
Shadow

Shugaba Buhari mutum ne me kunya, Ba ya son Fariya>>Rotimi Amaechi

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, shugaban kasa,Muhammadu Buhari mutum ne me kunya wanda baya son fariya.

 

Amaechi yayi wannan jawabine da yake bayyana dalilin da yasa shugaban bai je kaddamar da Layin Dogo na Itakpe-Warri ba, bayan da aka kammalashi.

 

Amaechi ya gayawa mawallafin Mujallar Ovation, Dele Momodu hakane a lokacin da suka yi wata ganawa.

 

Yace, yanzu an kammala aiki, saura kaddamarwa amma zuwa Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ya tsayar da komai.

 

Ya kara da cewa,kuma kasan shugaba Buhari mutum ne me kunya, baya son Fariya.

Karanta wannan  Ba zamu roki kungiyar malamai ta ASUU ta janye yajin aiki ba, iyayen dalibai suka mayarwa gwamnatin tarayya martani

 

Yace abinda shugaban yakan fada shine kawai a mayar da hankali wajan yin ayyuka yanda koda bayan basu mutane zasu ga irin nasarorin da suka samu amma wasu na son a rika zuwa kaddamar da ayyuka.

 

Yace sun yanke shawarar sakawa Layin dogon sunan tsohon shugaban kasa,Goodluck Ebele Jonathan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.