An bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauke gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele daga mukaminsa bayan ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Idan za ku tuna, Emefiele wanda ya sha musanta burin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, ya sayi fom din tsayawa takarar a ranar Juma’a.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnan babban bankin na CBN ya karbi fom din Naira miliyan 100 daga hannun sakataren jam’iyyar na kasa da kasa (ICC) da ke Abuja.
‘Yan Najeriya da suka mayar da martani kan wannan lamari sun ce ba bisa ka’ida ba ne a ce Gwamna CBN mai ci ya tsaya takarar ba, don haka ya kamata ya yi murabus ko kuma a tilasta masa yin murabus.