Yanzu haka shugaban kasa, Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar iyayen kasa dake gudana a fadarsa.
Mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnati, Boss Mustapha, me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno, da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari na cikin wanda suka halarci taron.
Akwai kuma tsaffin Shuwagabannin kasa irin su Abdulsalam Abubakar, da Goodluck Jonathan, da Yakubu Gowon.
Akwai kuma wasu gwamnonin Najeriya.
Babu dai cikakken bayani kan abinda ake tattaunawa a taron amma ana tsammanin ba zai wuce matsalar tsaro ba.