Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Jihar Kano a safiyar Litinin.
Shugaban ya je Kano ne domin ƙaddamar da bikin makon rundunar sojin sama ta Najeriya inda rundunar ke cika shekara 58 da kafuwa.
Rahotanni daga jihar na cewa an jibge jami’an tsaro masu ɗumbin yawa a sassa daban-daban na jihar sakamakon zuwan shugaban.

