Shugaban kasar Najeriya, muhammadu Buhari da Tinubu da Peter Obi sun jinjinwa Tobi Amusan yar wasan tseren Najeriya bayan ta lashe kyatar Gold a gasar ta Duniya bakidaya.
Bugu da kari Tobi ‘yar shekara 25 ta lashe wannan kyautar ne cikin salo inda ta zamo mace ta farko a duniya data tsalleke sandar da ake sawa a tseren cikin dakikai 12.12 a wasan kusa dan karshe.
Kuma bayan wannan ta sake kafa wani tarihin inda ta tsalle sandar a cikin dakikai 12.6 a wasan karshe na gasar kuma ta lashe kyautar naira miliyan 100.
Yayin datayi kukan murna bayan da aka saka mata taken kasa Najeriya.