Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aikewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da sakon ta’aziyyar hadimansa 2 da suka rasu a hadarin da ya faru dashi.
Hadarin ya faru ne a Abuja yayin da Jonathan ke tafiya daga filin jirgin sama zuwa gidansa dake Abuja, saidai shi bai jikkata ba.
Shugaba Buhari a sakon da ya aikewa da Jonathan yace yana fatan Allah ya bashi hakurin rashin da yayi da iyalan mamatan, sannan su kalli rasuwar ‘yan uwan nasu a matsayin bautar kasa.
Yace wannan kada yasa Jonathan yayi kasa a gwiwa wajan ci gaba da tafiye-tafiyen da yake na kawo zaman lafiya a ciki da wajen Najeriya.