fbpx
Friday, July 1
Shadow

Shugaba Buhari ya amince da Biliyan 3 dan gina titin Dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri

Gwamnatin Najeriya ta amince da sake gina titin jirgin ƙasa daga Maiduguri na JIhar Borno zuwa birnin Fatakwal na Jihar Rivers.

Ministan Sufuri Chibuke Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan ga manema labaran fadar gwamnati a yau Laraba, inda ya ce za a kashe dala biliyan uku (3,020,279,549) – kwatankwacin fiye da naira tiriliyan ɗaya.

“An amince da shimfiɗa layin dogo daga Maiduguri zuwa Fatakwal.,” in ji Amaechi, cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa.

Idan har aka aiwatar da aikin, zai zama layin dogo mafi tsayi a Najeriya wanda zai kai tsawon kilomita kusan 1,500 – ko kuma tafiyar kwana ɗaya cur babu tsayawa a mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published.