fbpx
Wednesday, March 3
Shadow

Shugaba Buhari ya amince da sake gina garuruwan Benuwai da makiyaya suka lalata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake gina garuruwan da Fulani makiyaya suka lalata a jihar Benuwe da sauran jihohin da abin ya shafa a kasar.

An kafa kwamitin da Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta kuma aka ba shi umarnin nemo hanyoyin samar da walwala da sauran kayayyakin da ake bukata a wadannan al’ummomin.

Wannan na daya daga cikin mahimman tattaunawar taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) na wata-wata wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja a ranar Alhamis kuma Mataimakin Shugaban kasar ya jagoranta.

An kuma yi wa Majalisar bayanin ayyukan mambobin kungiyar 10 da aka kafa a taron ta na karshe kuma sun hada da Mataimakin Shugaban kasa a matsayin Shugaba da gwamnonin jihohi tara don samar da mafita mai dorewa ga rikicin manoma da makiyaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *