Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhafi a ranar 28 ga watan Yuli ya bayar da naira biliyan 1.4 don siyawa gwamnatin Nijar motoci.
Kamfanin siyar da mota na Kaura ne aka baiwa wannan kwangilar ta sayan manyan motocin guda goma irinsu Toyota Land Cruiser V8.
Ganin wannan labarin yasa al’ummar Najeriya na sukar gwamnatin ta Buhari domin kasar na fama da wasu matsalolin daya kamata a gyara amma ta bayar da kyautar wa’yan nan makudan kudaden.
Inda har wasu dalibai ke cewa ASUU ya kamata ya baiwa kudaden domin su janye yajin aiki su samu su koma makaranta.
Kuma a kwanakin baya gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa tattalin arzikin kasar nana yayi kasa sosai ta yadda har batada kudin da zata yi aiki a shekarar 2023.