Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yayi kokarin hana gwamnoni da Ministoci sakawa ayyukan da suka yi sunansa amma gwamnan Kogi, Yahya Bello ya ki yi masa biyayya akan wannan umarni.
Shugaba Buhari ya bayyana hakane a jawabin da yayi a wajan ziyarar da ya kai jihar Kogi a gidan talabijin din Arise TV, Kamar yanda Daily Post ta ruwaito.
Shugaba Buhari ya kaddamar da ayyukan da suka hada da Jami’a da Asibiti da sauransu a jihar ta Kogi.