Shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari ya bayyana dalilin dayasa yaki zabar wanda yake so ya maye gurbinsa a zaben shekarar 2023.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ziyarar daya kaiwa mai martaba sarkin jihar Katsina, Alhaji Abdukmumini a hutun Sallah dayaje Daura.
Inda yace dalilin shine an kawo masa sunayen mutane talatin ya zaba daya a cikinsu kuma duk yawancinsu ministocinsa da gwamnoni.
Sannan kuma a gaban mataimakinsa Osinbajo ake yin komai, saboda haka bai da zabi don shi na kowa ne sai yasa ya bar deliget suka zabi wanda suke so.
Imda a karshe Asiwaju Bola Ahamd Tinubu yayi nasara.