fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Shugaba Buhari ya cika shekaru 75 a Duniya

A yau Lahadi, shugaban kasa, Muhammadu Buhari yake cika shekaru 75 da haihiwa, muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru da lafiyaa masu albarka.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ga kadan daga cikin tarihinshi:
An haifi Shugaba Muhammadu Buhari ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942 a garin Daura na jihar Katsina, sunan mahaifinshi Adamu mahaifiyashi kuma Zulaihat, shine na ashirin da uku a gidansu, mahaifinshi ya rasu yana da shekaru kusan hudu a Duniya,  yayi makarantar Firaimare a garin Daura da kuma Mai’adua kamin daga baya yaje makarantar Katsina Model School a shekarar 1953 da kuma Katsina Provincial School wadda yanzu ake kira da Government College Katsina daga shekarar 1956 zuwa 1961.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shiga makarantar horas da sojoji wadda ake kira NMTC a takaice a shekarar 1961, wadda a shekarar 1964 aka karawa makarantar girma zuwa ta horar da manyan jam’ian sojoji da ake kira da NDA a takaice.
A ahekarar 1971, shugaba Buhari ya auri matarshi ta farko wadda ake kira da suna Safinatu, sun samu ‘ya’ya biyar da ita, diyarsu ta farko sunan mahaifiyar Buhari aka saka mata watau Zulaihat, sai kuma Fatima, sai Musa wada Ya rasu sai Safinatu da kuma Hadiza. Shugaba Buhari ya saki matarshi Safinatu a shekarar 1988.
A shekarar 1989 shugaba Buhari ya auri A’isha Halilu wadda itace suke tare har yanzu, kuma sun haifi ‘ya’ya Biyar, A’isha, Halima, Yusuf, Zahara sai Amina.
Shuga Buhari ya taba zama gwamnan yankin Arewa maso gabar a shekarar 1975 sannan kuma ya taba zama gwamnan jihar Borno a shekarar 1976 duk karkashin mulkin soja.
Shugaba Buhari ya mulki Najeriya karkashin mulkin soja a shekarar 1983 zuwa 1985 bayan da yayi juyin mulki.
A shekarar 2015 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya neman takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar APC, lokacin da musamman Arewa ke cikin tashin hankalin kungiyar Boko Haram, Bom na tashi nan da can, shugaba Buhari ya lashe zaben shugaban kasar da akayi a shekarar 2015 kuma shugaban kasar wancan lokacin, Goodluck Jonathan yayi halin dattako inda, babu ja, ya kira shugaba Buhari ya tayashi murnar lashe zaben, a lokacin da ake dar-dar da tunanin abinda ka iya kai ya kawo.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *