Wednesday, June 3
Shadow

Shugaba Buhari ya cika watanni 3 cur ba tare sa fita kasar waje ba

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya cika Watanni 3 ba tare sa da yayi tafiya zuwa wata kasar waje ba.

Hakan kuwa ya farune watakila saboda matsalar cutar Coronavirus/COVID-19 data mamaye Duniya. Idan wannan lokaci bai zama mafi tsawo da shugaban ya tsaya a Najeriya ba tare da yin tafiya kasar waje ba tun hawansa mulki a shekarar 2015 ba to yana daya daga ciki.

 

Saidai a irin wannan lokaci da ake tsammanin zamansa a gida zai saka mutane su rika ma’amala dashi sosai ko kuma ya zagaya cikin kasa, ba’a samu damar hakan ba saboda cutar Coronavirus ta hanashi ganawa da mutane Sosai.

 

Da dama dai kan caccaki shugaban kasar saboda tafiye-tafiyen da yake zuwa kasashen waje wanda suke ganin kamar sun yi yawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *