Me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau kan mulkin kasarnan kusan ko wane yanki ana fama da tashin-tashina amma zuwa yanzu an samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a kusan ko’ina a kasarnan.
Kwanannan aka taso da wata maganar cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da mukamai a gwamnatinshi ga ‘yan yankin Arewa fiye da ‘yan yankin kudu, hakan yasa mukarrabanshi keta fito da bayanai masu karyata hakan.