Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sakawa rigistar ta’aziyyar mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alex Ekweme hannu a yau, a lokaci guda kuma ya jagoranci zaman majalisar zartarwa wanda aka dagashi daga jiya zuwa yau bayanda jiyan ba’a samu kammala zaman ba kamar yanda aka saba.