Shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari ya jinjinawa dakarun tsaronsa da suka kora ‘yan ta’addan da suka kawo masu farmaki a jihar Katsina.
A jiya ne dakarun tsaron nasa tare da ‘yan jarida da sauransu suka tafi daga Abuja zuwa Daura kafin zuwan shugaban kasar.
Shugaba Buhari zai yi Sallar sane a jiharsa ta Katsina a garin Daura, kuma yayi Allah Wadai da bata garin da suka kaiwa tawagar tasa harin.
Hadimin shugaban kasar, Garba Shehu ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter kuma yace mutane biyu da suka samu rauni suna jinya a asibiti.