fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Shugaba Buhari ya jinjinawa shugaban BUA bayan Kasar Faransa ta sake zabe shi a matsayin shugaban kasuwancinta da Najeriya

Shugaban kasar Najeriya, Mejo janar Muhammadu Buhari ya jinjinawa shugaban kungiyar BUA, Abdul Samad Rabi’u bayan shugaban kasar Faransa,

Emmanuel Macron ya sake zabar shi a matsayin shugaban kungiyar kasuwanci tsakanin Najeriya da Faranansa.

Shugaba Buhari jinjina masa ne a sakon daya fito daga hannun hadiminsa Garba Shehu wanda yayiwa taken, ‘Buhari na taya shugaban kungiyar BUA murna a sake zabar shi da Faransa tayi na shugaban kasuwancinta da Najeriya.

Inda yace shugaba Buhari ya jinjina masa saboda hazakarsa da kuma aiki tukuru yasa aka zabar shi a matsayin shugabar kungiyar wadda aka kaddama shekara guda data gabata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.