Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar Kano inda ya kaddamar da ayyuka daban-daban da gwamnatin jihar tayi, karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, bayan kammala ziyarar, shugaba Buhari ya tafi mahaifarshi, garin Daura, inda zaiyi hutun karshen mako acan.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka mai rakiya.
Kamin barinshi jihar Kanon, a ganawar da yayi da shuwagabannin jam’iyyar APC shiyyar jihar, sun bayyanamai cewa, a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu shine zabinsu, haka kuma a jihar Kano gwamna Gandujene zabinsu, shuwagabannin jam’iyyar sun bayyana cewa zasu siyawa shugaba Buharin fom din takarar shugaban kasar da kudinsu, kuma, cikin raha, gwamna Umar Ganduje yace, idan ma shugaba Buharin bai yarda ya tsaya takara ba to zasu iya kaishi kotu.
Amma shugaba Buharin bai basu amsar cewa ya amince ko bai aminceba, ya daiyi murmushi kawai.
Wasu karin ayyuka da shugaban kasar ya kaddamar a jihar ta Kano kamin ya wuce Daura sune katafaren kamfanin yin mai na Gerawa, wanda rahotanni suka bayyana cewa, shine mafi girma a Africa ta yamma da kuma kamfanin sarrafa shinkafa na Fullmark.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});