Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tsawaita mukamin shugaban Civil Defence, Abdullahi Gana Muhammadu da shekaru 5.
Abdullahi Gana ne da kansa ya bayyana haka a yayin da yake bikin cika shekaru 5 akan mukamin. Ya bayyana cewa yana fatan wannan tsawaitawar mukami da shugaba Buhari ya masa ta amfani ma’aikatar ta Civil Defence.
Me magana da yawunsa, Okeh Emmanuel ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda yace shugaba Buhari ta hannun ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya kara mukamin nashi.
Yace yana fatan za’a hada hannu dan ciyar da hukumar gaba.