Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a yau ranar juma’a shuwagabannin kamfanin BUA suka kai masa ziyara a fadarsa dake babban birnin tarayya.
Shugaba Buhari da kansa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.
Inda yace shugaban kamfanin Abdulsamad Rabiu ne ya jagoranci tawagar tasa kuma ya matukar ji dadin wannan ziyarar tasu.
Buhari ya yace Najeriya na matukar alfahari da kamfanin nasu domin yana kawo mata cigaba sosai.