Saturday, March 28
Shadow

Shugaba Buhari ya killace kansa kuma yana tari akai-akai duk da cewa gwaji ya nuna bashi da Coronavirus/COVID-19

Bayan da aka tabbatar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,  Abba Kyari na da cutar Coronavirus/COVID-19 an yiwa shugaban kasa,Muhammadu Buhari gwajin cutar amma shi gwajin ya nuna bashi da cutar.

 

Saidai Duk da haka Sahara Reporters sunce wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana musu cewa shugaba Buharin ya killace kansa sannan kuma yawan tarin da yake ya saka mutane da yawa na kusa dashi damuwa.

 

Hakanan an shirya gurin kebewar cutar Coronavirus/COVID-19 a cikin fadar shugaban kasar.

 

Cikin wanda Abba Kyari yayi mu’amala dasu bayan dawowa daga Jamus da kasar Egypt akwai Aliko Dangote da shugaban ‘yan sanda, Muhammad Adamu da gwamnonin Katsina dana Kogi.

 

A zuwa yanzu dai mutane 44 ne suka kamu da cutar a Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *