fbpx
Monday, August 15
Shadow

Shugaba Buhari ya nada sabon mataimakinsa na majalissar tarayya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Honourable Nasiru Baballe a matsayin sabon mataimakinsa na majalissar tarayya.

Hadimin shugaban kasar Garba Shehu ne ya bayyana hakan inda yace shugaban kasa yace Nasiru babban dan kasuwa ne na gari kafin ya shiga harkar siyasa.

Honourable Nasiru Baballe ya kammala karatunsa ne a kasar Ingila kafin ya dawo gida Najeriya, kuma a zaben 2011 da 2015 shine dan majalissar dake wakiltar karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Yayin da yanzu zai maye gurbin Ibrahim El Yakub wanda shi yanzu shugaban kasar ya bashi mukamin minista.

Leave a Reply

Your email address will not be published.