fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Shugaba Buhari ya nada sabuwar mai bashi shawara akan harkar siyasa

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Dr. Habiba Muda Lawal a matsayin sabuwar mai bashi shawara akan harkar siyasa.

Dr. Habiba ta kasance tsohuwar sakatariyar ma’aikatar muhalli, kuma kafin tayi ritaya ta samu lambar yabo sosai bisa namijin kokarin data yi a aikin nata.

Dr. Habiba Lawal ya kammala karatunta na Chemistry a jami’ar Ahmadu Bello ne dake Zaria kuma ta lashe kyautuka a jami’ar wanda suka hada da gwarzuwar daliba a lokacin data ke aji biyu da dai sauran su.

Sannan tanada shaidar karatu akan ilimin inganta rayuwar mata a jami’ar Landan dake Norwich.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.