Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da alkali Olukayode Ariwoola a matsayin shugaban alkalan Najeriya na wucin gadi
Alkalin kotun kolin, Olukayode Ariwoola ya karbi rantsarwar da shugaba Muhammadu Buhari yayi masa a majalisar sa dake babban birnin tarayya Abuja ranar litinin.
Kuma Alkalin dan shekara 62 ya karbi kujerar ne wurin Tanko Muhammad, kuma ya sha alwashin yin adalci tare da kare kudin tsarin mulkin Najeriya.