Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya roki bankin Duniya dana hadin kan kasashen Africa da sauransu dasu cika alakawarin da suka yi na bayar da Dala Biliyan $19.
Kudin dai za’a yi amfani dasu ne wajan farfado da tafkin Chadi, shugaba Buhari yace tafkin Chadi na kafewa, dan haka ya kamata wanda suka yi alkawarin su bayar da kudin.
Hakanan kudin za’a yi amfani dasu wajan farfado da harkar noma da dasa itatuwa da kuma yakar gurbacewar yanayi.
Shugaban yayi wannan maganar ne ranar Litinin a wajan taron majalisar dinkin Duniya dake wakana a birnin Abidjan na kasar Kwadebua.
Kasashe 11 ne suka taru wajan wannan taron inda suke tattauna yanda za’a kashe wadancan kudade idan sun shigo hannu.