fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Shugaba Buhari ya roki majalissar dinkin duniya ta yafewa Najeriya bashi, kuma za ayi zaben adalci a shekarar 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki majalissar dinkin duniya cewa ta yafewa Najeriya bashin data ke binta.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a taron majalissar dinkin duniya karo na 77 da suka gudanar a birnin New York dake kasar Amurka.

Inda yace wannan shine kari na karshe da zai wakilci Najeriya a wannan taron domin wata fuskar zasu gani daban a taron su na 78 da zasu gudanar.

Saboda haka ne yake so yayi amfani da wannan damar ya roki a yafewa Najeriya bashi, sannan kuma yayi alkawarin gudanar da zabe ba magudi a shekarar 2023 domin yana so ya kafa tarihi na adalci ko bayan ya sauka.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.