Shugaba Buhari ya sake nada Prof. Mojisola Adeyeye a matsayin shugabar hukumar kula da Abinci da magunguna ta kasa watau, NAFDAC.
Zata rike mukamin ne a karo na biyu kuma na karshe wanda zata shafe shekaru 5 akai.
Sakataren gwamnatin tarayya, Mr. Boss Mustapha ne ya kaiwa Prof. Mojisola Adeyeye wannan sanarwa.
Kuma sabon aikin nata ya fara ne daga 1 ga watan Disamba na shekarar 2022.
Me kula da yada labarai na hukumar, Dr. Abubakar Jimoh yace an tsawaitawa Adeyeye mukamin nata ne saboda yanda ta samu nasarori a shekarun baya.