fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Shugaba Buhari Ya Sanya Sunayen Tashoshin Jiragan Kasa Ga Tinibu, Osinbanjo Da Soyinka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya sunayen tashoshin jirgin kasa a layin Legas zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Ajaokuta zuwa Warri ga yan Najeriya da suka cancanta, in ji Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Daya daga cikin masu taimakawa shugaban kasa, Tolu Ogunlesi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wani twitter.
A cewar Ogunlesi, an sanya sunan tashar ta Apapa ne ga Bola Ahmed Tinubu, yayin da aka Sanya wa tashar Agege ga Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.
Sauran mutanen da aka sanya sunayen su ga tashar jirgin sun hada da Lateef Jakande (tashar Agbado), Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo (tashar Kajola), da Funmilayo Ransome-Kuti (tashar Papalanto).
Marigayi Mobolaji Johnson (tashar Ebute Metta), Wole Soyinka (tashar Abeokuta) Segun Osoba (tashar Olodo), Ladoka Akintola (tashar tashar Omio-Adio), Obafemi Awolowo (tashar Ibadan), Alex Ekwueme (Cibiyar Gudanar da Ayyuka).

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Gwamnoni zasu gana da shugaba Buhari ranar laraba kan matsalolin kasa musamman tattalin arziki

Leave a Reply

Your email address will not be published.