Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a kasar Jordan, inda yaje domin halartar taron gano hanyar magance ayyukan ta’addanci, wani abu dayabirge mutane da wannan tafiya ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, shine, bayan jirginshi ya sauka a kasar Jordan, kamin ya sauka daga cikin jirgin, saida ya juya, ya gayawa matukin jirgin nashi cewa, Nagode.
Gwamnonin Osun, Kogi da Naija da kuma wasu manyan ma;aikatan gwamnatine suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari rakiya zuwa kasar ta Jordan.
Muna fatan Allah yasa su gama abinda suke su kuma dawo gida Lafiya.