Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnan jihar kogi, Yahya Bello a fadarsa dake Abuja.
Shugaban ya shiga ganawar ne bayan da Yahya Bello ya bayyana cewa baya tare da gwamnonin Arewa dake goyon bayan a tsayar da dan kudu takarar shugaban kasa a APC.
Ana tsammanin a ganawar tasu shugaba Buhari zai yiwa gwamna Yahya Bello magana ne kan lamarin.