fbpx
Monday, August 8
Shadow

Shugaba Buhari ya tsawaita hana zirga-zirga a Legas, Ogun da Abuja

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya tsawaita dokar hana zirga-zirga a jihohin Legas da Ogun da babban birnin tarayya Abuja zuwa wasu kwanaki 14.

 

Shugaban ya bayyana cewa ya dauki wannan matakine bisa rahoton da ya karba daga kwamitin daya kafa na yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Shugaban ya nemi hadin kan mutane wajan hada hannu da gwamnati a yaki wannan cuta.

 

Shugaban yace wannan ba maganar wasa bace harkace data shafi rayuwar da mutuwa, Saudiyya sun rufe Masallatai, Paparoma bai yi taron Easter ba, kasashen India da Italiya da Faransa duk a kulle suke kuma sauran kasashen ma na bin sahu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

  • Abbati Muhammad Yaba

    Mudai muna kira da shugaban kasa da yaduba talakawa wallahi tallafinnan haryanzu baisu indamukeba mutalakawa musamman mutanen babban barnin nigeria Abuja。

Leave a Reply

Your email address will not be published.