fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Shugaba Buhari yace bazai taba mantawa da sadaukarwar da masoyanshi suka maiba

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bazai taba mantawa da irin sadaukarwar da jajircewar da ‘yan Najeriya suka nuna ba wajan bayar da gudummuwarsu a zaben shekarar 2015 daya bashi damar zama shugaban kasa ba.

Buharin ya bayyana hakane a lokacin da yake amsar bakuncin wata kungiyar goyon bayan gwamnati da suka kaimai ziyara fadarshi a yau Juma’a, haka kuma ya kara dacewa irin wahalhalun da ‘yan Najeriyar sukasha na tsawon lokaci da kuma jajircewar da suka nuna ba zasu taba tafiya a banzaba, ‘ya’ya da jikoki da zasuzo nan gaba zasu godemusu bisa hakan.
Kuma ya bukaci ‘yan Najeriyar dasu cigaba da kasancewa na gari kuma masu jajircewa akan gaskiya, ya kumace yana sane da dama sun saka kawunansu cikin hadari domin ganin sun bayar da gudummuwar data kamata dan cigaban kasarmu, saboda haka yana matukar godiya, bazai taba mantawaba.
Yace irin barnar da ya iske a gidan gwamnati abin ya wuce tunani, yace yayi mamakin yanda har Najeriya ta kawo zuwa yanzu a irin wancan gurbataccen tsarin da aka rika tafiya akanshi, ya kara da cewa ikon Allahne kawai yasa Najeriyar ta dore har zuwa yanzu.
Wannan jawabi yana cikin wata sanarwar bayan ganawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da kungiyar goyon bayan gwamnatin da me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin watsa labarai Femi Adeaina ya fitar.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *