fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Shugaba Buhari yace kasar Libya ce ta kawo matsalar tsaro a Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin zaman lafiya a kasar Libya ne yasa Najeriya da Sahel ke fama da matsalar tsaro.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne bayan kwamishinan kasar Canada dana Mexico, Ambasada James Kingston Christoff da Ambasada Juan Alfred Miranda Oritz sun aikowa Najeriya wasikar amincewa su hada kai a magance matsalar tsaro.

Inda yace yana godiya a garesu da kuma jinjina bisa goyon bayan da suka nuna na magance matsalar tsaro bama a kasashensu kadai ba, amma a Duniya bakidaya.

Karanta wannan  Bideyo: Ronaldo baiji dadin ajiye shi a benci ba da Yen Hag yayi

A jiya ranar talata ne hadiminsa Femi Adesinan ya bayyana hakan, kuma yace wannan hadin kan zai taimaka sosai wurin kawo karshen matsalar tsaro a kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.