Gwamnatin tarayya tace tana iya bakin kokarinta wurin ceto sauran fasinjojin jirgin kasa na jihar Kaduna dake hannun ‘yan bindiga.
Mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin dayake ganawa da manema labarai na BBC Hausa.
Inda yace gwamnatin ta biyawa ‘yan ta’addan dukkan bukatunsu saboda haka bai kamata ace basa yin kokarin akan wannan lamarin ba.
Inda yace shugaban ‘yan bindigar yace a sako masa matarsa mai ciki, kuma gwamnati ta sakota bayan tayi dawainiyar haihuwarta.
Sannan ya sake cewa a sako masa yaransa dake gidan kurkuku shima gwamnatin tayi hakan a jirgin sama akai masa su, saboda haka suna iya bakin kokarin su.