A yau Talatane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara wata ziyarar kwanaki biyu a jihar Ebonyi, jirgin saman shugaban kasar ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa me suna Akanu Ibiam dake jihar Enugu inda gwamnonin jihohin Enugu da Ebonyi da Imo da Kogi da kuma tarin jama’a suka suka tarbeshi.
Daga nan shugaban kasar ya zarce zuwa Ebonyi inda nanne zai fara ziyarar kafin gobe ya wuce Anambra .
An baiwa shugaban kasar wata sarautar gargajiya me suna Enyioma 1 of Ebonyi, wadda rahotanni suka bayyana cewa tana nufin Abokin kowa, wasu kuma sun fassara sarautar da cewa tana nufin abokin mutanen Ebonyi.
Shugaban kasar ya bude wata katafariyar gadar sama da aka gina a jihar ta Ebonyi, haka kuma an bashi kyautar goro, gobene ake saran zai wuce jihar Anambra ifan Allah ya kaimu.