Kakakin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa shugban kasa, Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren dake faruwa.
Yace shugaban zai tabbatar da cewa rikice-rikicen basu yadu zuwa wasu sauran gurare ba. Ya bayyana hakane a wata ganawar da yayi da Channelstv.
Garba Shehu yace sai an hada hannu da jami’an tsaro da shuwagabannin al’umma da duk wani me ruwa da tsaki dan kawo karshen matsalar.