fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin da ‘yan Bindiga suka kai jihar Adamawa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da ‘yan Bindiga suka kai jihar Adamawa.

 

‘Yan Bindigar sun kai harinne a garin Mubi na jihar inda suka harbi Rev. Daniel Umaru da kuma kashe ‘ya’yansa 2 da kuma sace diyarsa.

 

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda yaje yiwa iyalan mamatan ta’aziyya.

 

Ya bayar da tabbacin cewa, gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba wajan kama wadanda suka aikata wannan laifi dan hukuntasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.