fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin Kaduna inda ya jajantawa wanda lamarin ya rutsa dasu

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai jihar Kaduna da ya kashe mutane da dama a Ranar Lahadin data gabata.

Wannan na kunshene a cikin wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar,Malam Garba Shehu ya fitar ga manema labarai.

Shugaban yace a bayyane yake wannan hari da ‘yan bindigar suka kai suna nuna fushinsu ne akan mutanen da basu ji basu gani ba saboda matsa musu da hare-hare da jami’an tsaro suka yi a dazukan Birnin Gwari fa Kaduru.

Karanta wannan  Na So A Ce Ana Kai Ziyara Lahira, Da Na Ziyarce Ki, Cewar Matashin Da Budurwar Sa Ta Rasu Ana Dab Da Aurensu

Yace babu wani abu da ‘yan bindigar za su yi da zai hana gwamnati murkushe su dan kiwa ba zasu rika kaiwa mutane hari ba tare da an murkushesu ba.

Shugaban ya jajantawa wanda lamarin ya rutsa dadu inda kuma ya baiwa gaba dayan ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnati zata dukufa dan ganin ta kawo karshen ‘yan ta’adda a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.