fbpx
Friday, June 9
Shadow

Shugaba Buhari yayi fatan Allah ya baiwa Ministan harkokin waje da ya kamu da Coronavirus/COVID-19 lafiya

A dazu ne muka ji yanda Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 kuma ya tafi killace kanshi.

 

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi mai addu’ar samun sauki. Shugaban a cikin wani sako daya fitar ta shafinshi na Twitter yace Ministan Mutumin Kirki ne kuma Najeriya tana gode masa saboda kokarin da yake.

Shugaban ya bayyana cewa ministan yana kokari sosai wajan ganin an kawar da cutar Coronavirus/COVID-19 dan habaka tattalin arzikin Najeriya.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *