fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Shugaba Buhari yayi watsi da Tinubu, zai goyi bayan Jonathan ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023

Wata Majiya ta bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi watsi da Tinubu, zai goyi bayan Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara a shekarar 2023.

 

Majiyar ta Sahara Reporters ta bayyana cewa, maimakon Tinubu ko Osinbajo da ake tsammani, tuni shugaba Buhari ya fara shirin goyawa Goodluck Jonathan baya a 2023.

 

Majiyar ta kara da cewa, tuni wasu ‘yan siyasa daga Arewa suka yi na’am da wannan mataki.

 

Wannan mataki dai a cewar majiyar, kokarine na ganin an baiwa Goodluck Jonathan damar kammala wa’adinsa na 2 da bai samu yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.