fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Shugaba Buhari zai kai ziyara kasar Kwadebuwa

Ranar 28 da ranar 29 ga watannan na Nuwamba da muke ciki idan Allah ya kaimu, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Kwadebuwa inda zai halarci taron gamayyar kungiyoyin tarayyar turai dana tarayyar Afrika, taron wanda za’a tattauna batun saka jari a harkar matada dan samun ci gaba me dorewa zai samu halartar shuwagabannin kasashen nahiyar turai dana nahiyar Afrika.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaba Buhari, bayan taron zai kuma halarci wata liyafar cin abinci da kasar ta kwadebuwa zata shiryawa shuwagabannin.

Cikin wadanda zasu yiwa shugaban rakiya akwai gwamnonin jihohin Bauchi dana Akwa-Ibom da sauran manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministoci.
Wannan bayani yana kunshene a cikin wata sanarwa da me baiwa shugaban shawara ta fannin watsa labarai Femi Adesina ya fitar a tau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Muma Buhari yawa Abbbinmu Annabi Isa(AS) batanci>>Inji Wani Fasto

Leave a Reply

Your email address will not be published.