Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki jihar Kaduna a tsakanin ranar Alhamis da Juma’a idan Allah ya kaimu.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Asabar.
Shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamna Malan Nasiru Ahmad El-Rufai yayi a yayin ziyarar tasa.
A baya dai shugaba Buhari ya kai irin wanna ziyara jihar Ogun.